-->
Memphis Depay ya koma atisaye a Lyon bayan jinyar watanni shida

Memphis Depay ya koma atisaye a Lyon bayan jinyar watanni shida

Memphis Depay ya koma yin atisaye a kungiyarsa ta
Olympique Lyon kamar yadda ta sanar.
Wannan ne karon farko da dan kwallon tawagar Netherlands ya
fara taka leda tun bayan jinyar wata shida.
Man City da Chelsea na zawarcin Chilwell..
Memphis Mai shekara 26 tsohon dan wasan PSV da
Man United ya ji rauni ranar 15 ga watan Disamba a
gasar Ligue 1 Da Stade Rennes.
Ranar Litinin Depay ya je Lyon don likitoci su auna koshin
lafiyarsa don ci gaba da karbar horon tamaula da tuni Lyon ta
fara atisaye a makon jiya.
Kungiyar na shirin fafatawa a gasar Champions League da za a
ci gaba, inda ta ci Juventus 1-0 a wasan farko na zagayen
kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.
Komawa atisaye da Depay ya yi batu ne da zai karawa Lyon
kwarin gwiwa.

0 Response to "Memphis Depay ya koma atisaye a Lyon bayan jinyar watanni shida"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel